Wai! Tsinken sigari biliyan 20 yan Nijeriya ke sha ko wani shekara
Yace a cikin shekarar 2015 asarar da shan taba ya janyo ma kasar ya kai adadin dala biliyan 7.6. Ya kara da cewa akalla mutum sama da miliyan 4.5 ke ta'amali da taba yayin da kashi 86 cikin dari na daga cikin masu ziyartar wuraren shakatawa suna shakar hayakin taba.
Babban ministan kiwon lafiya, Farfesa Isaac Adewale ya sanar cewa akalla tsinken sigari biliyan 20 yan Nijeriya ke sha ko wani shekara.
Ministan ya bayyana hakan ne a wani taron da yayi da manema labarai na raya zagayowar ranar yin watsi taba na duniya a garin Abuja ranar litinin.
Yace a cikin shekarar 2015 asarar da shan taba ya janyo ma kasar ya kai adadin dala biliyan 7.6. Ya kara da cewa akalla mutum sama da miliyan 4.5 ke ta'amali da taba yayin da kashi 86 cikin dari na daga cikin masu ziyartar wuraren shakatawa suna shakar hayakin taba.
A ko wace ranar 31 ga watan Mayu ana gudanar da taro ne domin yin watsi da shan taba a fadin kasashen duniya.
Ministan yace a cikin ko wace dala daya da kamfanin taba take samu a matsayin riba, dala 3 ake kashewa wajen neman lafiyar kan ciwon da shan taba take haifarwa. Yace masana'antu dake sarrafa taba suna samun riba sosai sai dai ba sa daukan nauyin illar da tabar ke haifarwa a jikin dan Adam.
Maudu'in taron raya wanan ranar na bana shine "taba da ciwon zuciya" kuma Farfesa Adewale ya bayyana cewa akalla dala miliyan 800 Nijeriya take rasawa domin cutar ciwon zuciya da ciwon siga da bugun jini.
Ministan yace gwamnatin zata dau mataki kan kayan taba da ake sarrafawa ciki har shisha.
Leave a Comment